Labarai

Gwamnatin Sokoto zata rushe unguwar Karuwai da ake kira Raymond

Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewar zata rushe wata unguwar da batagari suka mayar da ita mafaka a jihar da ake kira da sunan ‘Raymond Village’.

Ita dai wannan unguwa bayanai sun tabbatar da cewar mafaka ce ta dukkan masu aikata laifi musamman ‘yan kwaya da Karuwai da sauran masu aikata laifuka.

Gwamnan jihar Sokoto Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ne ya bayyana haka a ranar Litinin bayan da yakai ziyarar bazata a unguwar sakamakon korafe korafe da suka yi yawa game da ta’addancin da ake yi a wajen, tuni dai rahotanni suka nuna cewar an rushe unguwar dake wajen birnin Sokoto.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: