Labarai

Gwamnatin Nijeriya Za Ta Maye Gurbin Matsayin BVN Da Katin Zama Dan Kasa NIN -Ministan Sadarwa Sheikh Pantami

Daga Comr Abba Sani Pantami

Ministan sadarwa da sabon tsarin gina tattalin arziki na zamani Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya ce gwamnatin tarayya tana kan hanyar maye gurbin matsayin BVN da katin shaidar zama dan kasa NIN.

BVN lamabobi ne na tantancewa da bankuna suke bawa kwastomominsu.

Tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN), Sanusi Lamido, ne ya bullo da tsarin BVN domin tsaftace harkokin bankuna da kuma magance badakala da cin hanci.

Hukumar bayar da katin shaidar zama dan kasa, NIMC, ce ke bayar da lambobin tantancewa na NIN ga kowanne dan kasa da ya yi rijista da gwamnati.

Da yake jawabi ranar Litinin yayin da ya kai ziyara domin ganin aikin rijistar dan kasa a Abuja, Pantami ya ce za’a koma aiki da NIN a bankuna, sabanin amfani da BVN.

“Tuni na ja hankalin majalisar koli ta bunkasa tattalin arzikin kasa da gwamnan babban bankin kasa (CBN) akan bukatar yin hakan.

“Na bashi hujjar cewa NIN ta fi BVN muhimmanci saboda ita ta kasa ce ba wani bangare daya kadai ba.

“An riga an kirkiri doka akan NIN, ita kuwa BVN tsarin banki ne kawai, wanda bashi da tasiri ko karfi fiye da dokar kasa,” a cewarsa.

Pantami ya kara da cewa komawa amfani da NIN zai tabbatar da samun karuwar tsaro da tsare sirrin bayanan ‘yan kasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: