Labarai

Gwamnatin Nijeriya Ta Kaddamar Da Sabon Tsarin Tsaron Intanet Don Bunkasa Tattalin Arzikin Kasar

Daga Comr Abba Sani Pantami

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci yin garambawul ga tsarin tafiyar da tsaron intanet ta hanyar da zai bunkasa hanyoyin tattalin arzikin kasa da ilimi da kuma dakile aikata laifuka.

Yayin da ya ke kaddamar da wani sabon shiri, shugaban ya bukaci ganin tsarin ya kunshi masu ruwa da tsaki a kan harkar intanet wadanda zasu bada hadin kai wajen tabbatar da tsaron kasa a intanet da kuma harkar sadarwa baki daya.

Buhari ya bayyana fatar ganin hadin kan ya taimaka wajen samun hanyoyin da zasu taimakawa ‘yan Najeriya cimma muradun kansu ta hanyar gudanar da harkokinsu ta intanet.

Shugaban ya ce gwamnati ta kaddamar da wasu sabbin manufofi wadanda za su inganta amfani da kafar intanet ga ‘yan kasa a kowacce rana sakamakon kaddamar da shirin fadada hanyar sadarwa ta kasa daga shekarar 2020 zuwa 2025 da tsarin takardun shaidar zama dan kasa da asusun ajiyar gwamnati na bai daya da kuma tsarin asusun ajiyar banki na BVN.

Buhari ya ce duk wadannan tsare tsare an yi su ne domin shawo kan matsalar tsaro da tattalin arzikin da suka addabi Najeriya, a daidai lokacin da ake samar da tsarin da zai tabbatar da gaskiya wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Shugaban ya ce tabbas Najeriya kamar kowacce kasa tana fuskantar matsalolin ta da suka shafi aikata laifuka ta yanar gizo da ayyukan ta’addancin da ke gudana yanzu haka, ta hanyar amfani da farfagandar da ‘yan ta’adda ke yi wajen yada kalamun batunci da labaran karya da kage da cin amanar kasa ta hanyar bata sunan jama’a ko kuma gwamnati.

Buhari ya ce ko a watan Oktobar bara Najeriya ta gamu da matsalar yadda aka yi amfani da intanet wajen yada labaran karya da kuma tinzira jama’a su yi bore, abinda ya haifar da zanga zangar da ta rikide ta zama tarzoma wadda ta kai ga rasa rayuka da kuma asarar dimbin dukiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: