Labarai

Gwamnatin Neja Ta Kaddamar da Kungiyoyin Sa Kai Domin Shawo Kan Matsalar Tsaro A Fadin Jihar

Daga Jamilu El Hussain Pambegua
Gwamnatin jihar Neja karkashin Gwamna Abubakar Sani Bello ta kaddamar da kungiyoyin sa kai domin dakile matsalar tsaro da ta addabi jihar.

Abubakar Sani Bello ya ce “wadannan kungiyoyi za mu yi aiki da su don magance matsalar daba da matasa ke yi da ya addabi garin Minna babban Birnin jihar”.

Ya kuma kara da cewa ‘yan sa kan za su shawo kan matsalar ‘yan bindiga da suka addabi wasu sassa na Jihar.

Kungiyoyin sa kan wadanda ke dauke da mutane 161, sun samu horaswa na mussaman har na tsawon sati biyu, cewar kwamanshinan ‘yan sandan jihar, CP Adamu Usman.

Gamayyar kungiyoyin sa kan sun hada da Chinnaka, Abidoka, ADC, Hunters Group, Vigilante, AOG, WAL Brigade, Maitunbi Security Organization da sauransu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: