Labarai

GWAMNATIN KANO ZATA GINAWA MALAMAI GIDAJE 5,000

Fassara daga Faizu Alfindiki.

Gwamnatin jihar Kano za ta gina gidaje kimanin 5,000 ga malamai a makarantun firamare da sakandare na gwamnati a jihar, a karkashin kashin farko na shirin da nufin samar da ingantattun masaukai ga malamai da iyalansu a jihar.

Shirin, wanda aka yiwa lakabi da Mazaunan Keɓe Malamai, za a aiwatar da shi ne tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar, da Family Homes Funds, da kuma Bankin Mortgage na Tarayya.

Gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakanne a taron masu ruwa da tsaki kan shirin da aka tsara a daren Asabar a gidan Gwamnatin Kano.

“Kowace karamar hukuma daga cikin karkara 36 za ta sami rukunin gidaje 100 yayin da ragowar kananan hukumomi takwas za su samu gidaje 150 kowannensu.

Gwamna Ganduje ya ce “Gwamnatin za ta samar da filayen, kayan taimako kamar ruwa, wutar lantarki da hanyoyi, yayin da sauran bangarorin kuma abokan harka za su kula da su ”Inji Gwamna Ganduje.

Gwamnan, duk da haka, ya nuna cewa shiga cikin shirin, wanda zai fara a shekara mai zuwa, akwai zabi kuma wadanda suka ci gajiyar za su biya gidajen a cikin sauki.

Ganduje ya kuma bayyana cewa “gwamnatina ta damu da tabbatar da wadatar malamai da kuma samun damar zuwa gidajensu don kar su zama cikin kunci yayin da suka yi ritaya daga aiki.”

Ya kafa kwamiti na fasaha (Technical Committee) a karkashin Hon. Rabi’u Sulaiman Bichi an kafa shi ne don tsara hanyoyin yadda za a gudanar da aikin cikin sauki tare da fitar da hanyoyin zamani.

A nasa jawabin, Hon. Sulaiman Bichi ya ci gaba da cewa, shirin samar da gidaje na malamai shi ne don inganta manufofin Ilimi na Kyauta kuma Tilas.

“Lokaci na karshe da aka gina wa malamai a Kano shi ne a zamanin Native Authority “, in ji shi.

A nasa bangaren, wakilin Family Homes Funds, Engr. Musa Shu’aibu Mukhtar ya bayyana cewa hukumarsa a shirye take ta hada hannu da gwamnatin jihar Kano don samar da ingantattun gidajen kwana ga malamai, inda ya kara da cewa aikin zai samar da dubban ayyuka a jihar.

Fassarawa daga #FaizuAlfindiki
Tsohon Mai bada shawara ga gwamna akan harkokin Jama’a.
13rd, disamba, 2020.
#Realuyusuf #FASM

Haarun

Haruna Lawan Usman is a certified Animal Health and Production Technologist, with more than 4 years experience in Animal Health and Production Technology.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: