Labarai

Gwamnatin Kano Za Ta Saya Wa Dalibi 500 Fom Din JAMB

Gwamnatin Kano a zamanta na majalisar zartarwar da aka gudanar a jiya Laraba ta amince da kashe Naira miliyan 37 don saya wa dalibai ‘yan asalin jihar da za su zauna jarrabar sharar fagen shiga jami’a fom din jarrabawar JAMB.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammadu Garba ne ya bayyana wa manema labarai hakan bayyan kammala zaman da majalisar zartarwar jihar kan gudanar a kowace Laraba
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin Kano ta amince da kashe wasu miliyan 30 din dai kuma wajen gyara makarantar Sakandire ta Dandalama da ke karamar hukumar Dawakin Tofa.
Har ila yau, majalisar zartarwar ta jihar Kano ta amince da kashe sama da Naira miliyan 247 don yin gyara ga titunan Niger, da Yoruba, da Hausa da Igbo duk a yankin Sabon Gari da ke karamar hukumar Fagge.