Gwamnatin Kano Ta Zabi Sarkin Kano A Matsayin Wanda Zai Kula Da Mukabala Tsakanin Sheik Abduljabar Da Malaman Kano
Daga Jamilu El Hussain Pambegua
Gwamnan jihar Kano, Dakta Ummar Abdullahi Umar Ganduje ya zabi Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero don kula da muhawarar da za a yi tsakanin Sheikh Abduljabar da Malaman Kano.
Sannan Gwamnatin ta Jihar Kano din ta zabi fadar Mai Martaba Sarkin Kano a matsayin wajen da za a gudanar da tattaunawar.
Gwamnan Ganduje ya ce “mun zabi fadar Mai Martaban ne tunda batu ne na addini”.