Gwamnatin Kano Ta Wanke Ado Doguwa Daga Zargin Kisa A Yayin Zaben 2023
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ta wanke dan majalisar tarayya na Tudun Wada da Doguwa Alhassan Doguwa daga zargin kisan kai.
A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar dauke dasa hannun Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista M.A Lawan ya ce babu dalilin da zai sa a cigaba da tuhumar Doguwa.
A cewar gwamnatin ta Kano ta ce ba za ta iya tuhumar Alhassan Ado Doguwa da laifin kisan kai ba sakamakon rashin isasshiyyar hujja.
Daga Salisu Magaji Fandalla’fih
Add Comment