Labarai

Gwamnatin Kano Ta Haramta Siyar Da Gida Ko Fili Ko Kuma Bayar Da Haya

Gwamnatin ta ce kada a siyar dko bayar da haya har sai an samu sahalewa daga hakimi ko wani wakilin sa.

Gwamnatin jihar Kano ta haramta siyar da gidaje da bayar da haya ga mutanen da bas u samu amincewa daga shugabannin gargajiya ba.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Usman Alhaji ya fitar wanda sakaten yada labaran sa ya fitar a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce an ɗauki matakin haka ne domin tsare rayuka da dukiyoyin al’umar jihar Kano.

Kuma haramta hakan zai taimaka wa jami’an tsaro wajen cimma nasarar yaƙi da ƴan ta’adda wanda aka tasamma yi haiƙan a halin yanzu.

Dokar da gwamnatin ta saka ita ce hana siyar da gida ko fili ko kuma bayar da haya har sai an smau sahalewa daga hakimi ko wani wakilin sa.

Sanarwar ta gargadi dillalai da masu bayar da hayar gidaje da siyar wa da su bi dokar domin taimaka wa tsaro ta yadda za a cimma nasarar wajen yaƙi da ta’addanci a ƙasa baki ɗaya.

Gwamnatin tarayya hadin gwiwa da gwamnatocin jihohi sun sake salo wajen yaƙi da yan bindiga wanda aka ɗauki tsawon lokaci ana fama da shi a jihohi daban-daban na ƙasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: