Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Sheikh Abduljabbar Kabara Da Yin Waazi Harma Da Tarurruka

0 0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Gwamnatin Kano Karskashin Jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta dakatar da Malam Abduljabbar Kabara da yin waaazi da kuma tarurruka da yake gabatarwa a Masallacinsa dake filin mushe a cikin kwaryar Kano.

Hakan ya biyo bayan yadda Malamin yake Batanci ga Manzan Allah (SAW) da kuma wasu daga cikin sahabbai kamar yadda akeji a cikin karatuttukanshi da kuma yadda yake suka ga Malaman Hadisi irinsu Imam Malik, Bukhari da kuma Muslim.

Malamai da dama sunsha yin kira da gwamnati data dakatar da Malamin bisa kalaman da yakeyi ka iya kawo rashin zaman lafiya  a jihar Kano.

Jawabi daga bakin Kwashinan Yada Labarai Na Jihar Kano

DOWNLOAD HERE

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 782

A wani Rahoton da muka samu kuma Wani Matashi Mai Suna Aliyu Yahaya Mai rajin kare martabar Manzan Allah (SWA) , Sahabbansa Allah ya kara musu yadda da kuma Malaman Musulunci ya shigar da kara akan dakatar da Karantarwar  da Malamin yakeyi wacce ta saɓa da koyarwar musulunci  kamar yadda ya rubuta a Shafinsa na Facebook.

 

#Babu gurin Zagin #Sahabbai  #Kano jiya kenan bayan kammala zaman mu na gaggawa da mai magana da yawun rundunar “yan sandan Kano akan Koken mu, da muka gabatarwa hukumar akan yadda #Abduljabbar Kabara, keson haddasa mummunar #hatsaniya a nan Kano. #Alhamdulillah kuma a jiyan #Gwamnatin Kano itama ta karbi kokemmu akan wancan dan Tashar inda ta umarci Rufe Masallacin tare da hanashi gudanar da duk wasu Sharholiya anan Kano.

#Alhamdulillah #Alhamdulillah #Alhamdulillah

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: