Labarai

Gwamnatin Kano ta ce, Abduljabar bai tuba ba!!!

Kwamishinan harkokin addinai na jihar Kano, Dr.Tahar Adam, (Baba Impossible)* ne ya baiyana haka.

A cewarsa sakon Muryar da *Abduljabar* ya fitar bata nuna cewar ya tuba ba, illa janyewar da yake cewa ya yi, Yace duk wanda aka samu da lefin batanci ga Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam to babu maganar tuba illa zartar da hukunci akansa.

Kwamishinan harkokin addinai na jihar Kano, yace a yanzu haka suna kan rubuta rahoton da zasu aikewa da mai girma gwamna Ganduje da shi domin daukar matakin da ya dace.

Daga nan sai yaja hankalin al’umma da su guji daukar doka a hannu domin gwamnati ba zata saurarawa duk wanda aka samu da yunkurin tada husuma ba.

#Tsanyawa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: