Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasir El-Rufa’i, Tana Gayyatar Yan Nijeriya, musamman mazauna jihar, zuwa wajen Gangamin Taron Murnar dawowar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da kuma kara jaddada goyon baya ga Gwamnatinsa.
Ana Gayyatar dukkanin Kungiyoyi dama dai-daikun mutane.
Kuma Ana kira ga dukkan Kungiyoyi da su taho da Banner wacce take dauke da sunan kungiyar tasu da kuma yankin da suka fito.
Za’a gudanar da wannan taro kamar haka:
Rana: Talata 22 ga watan Augusta, 2017.
Lokaci: 9:30 na safe.
Wuri: Murtala Square, Kaduna.
Allah yabada ikon zuwa. Ameen
Sanarwa daga Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, da kuma Mai bawa Gwamnan Shawara akan harkokin Siyasa, Malam Uba Sani.
Source In Jaridar Rariya
Add Comment