Daga Suleiman Abba (TBABA)
Gwamna Nasir Ahmad El-rufai ya kai ziyarar gani da ido ma’aikatar tsaro da harkar cikin gida na jihar Kaduna.
Inda Kwamishinan tsaro da harkokokin cikin gida, Samuel Aruwan ya nunawa Gwamnan kammala aikin sanya kyamarori da aka yi a fadin jihar.
Gwamna El-rufai ya yaba da nagartar aikin, wanda yana daga cikin alkawarin da Gwamnan ya dauka na kawo karshen ayyukan bata gari a jihar.