-Advertisement-


Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Gwamnatin Kaduna Ta Maka El-Zakzaky A Kotu, Tana Tuhumar Sa Da Laifin Kisa


0 516

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Gwamnatin Kaduna Ta Maka El-Zakzaky A Kotu, Tana Tuhumar Sa Da Laifin Kisa.

Gwamnatin Kaduna ta maka shugaban mabiya Shi’a, Sheikh Ibarhim El-zakzaky kotu, ta na zargin sa da laifin kisa.

An maka El-zakzaky kotu ne a daidai lokacin da mabiyan sa ke ta kara tururuwa a Abuja, su na zanga-zangar tilas sai an saki jagoran na su.

Lauyan sa Femi Falana ya ce an aika masa da sammacen karar da aka kai shehin malamin tun a ranar 18 Ga Afrilu, 2018.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 324

- Advertisement -

Idan ba a manta ba, tun cikin watan Disamba, 2016, kotun Najeriya ta bada umarnin a saki malamin, amma gwamnatin tarayya ta yi kememe da umarnin wanda kotu ta bayar.

Wannan cajin kisa da aka yi wa malamin har caje-caje takwas, ya zo ne bayan shi kan sa malamin ya rasa ‘ya’yan sa har guda shida, wadanda sojoji suka bindige a wurin zanga-zanga a Zariya.

A lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan, an kashe masa yara biyu, lokacin mulkin Buhari kuma a waki’ar Buratai an kashe masa ‘ya’ya hudu.

A zaman yanzu kuma ya rasa ido daya, yayin da dayan kuma ana ta kokarin fita waje da shi domin a yi masa aiki, amma gwamnatin tarayya ta ki sakin sa.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.