Labarai

Gwamnatin Kaduna ta haramta bumburutu a wasu sassan jihar

Gwamnatin jihar Kaduna ta a bayar da sanarwar haramta bumburutu a wasu kananan hukumomi a fadin jihar, kananan hukumomin da dokar ta shafa sun hada da Birnin-Gwari da Giwa da Igabi da Kajuru da kuma karamar hukumar Chikun.

Gwamnatin ta bayar da sanarwar ne ta bakin Kwamashina mai kula da lamuran tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan. Inda tace ta dauki wannan mataki ne domin gyara al’amuran tsaro da suka tabarbare a jihar.

Haka kuma, Gwamnatin ta haramta cin kasuwannin sati sati a wadannan yankunan kananan hukumomi har illa masha Allah.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: