Get New DJ Mixes
Labarai

Gwamnatin Jihar Legas Ta Ce Dole A kashe Manjo Al-Mustapha

Gwamnatin jihar Legas sun bukaci kotin koli da ta dakatada da hukunci da kotun daukaka kara tayi na sake Manjo Hamza Al-Mustapha, jami’in tsaron tsohon shugabankasar Najeriya, marigayi Janar Sani Abacha da Alhaji Lateef Shofolahan akan kisan Alhaja Kudirat Abiola.

Gwamnatin Legas ta yi kira da kotun koli da ta zantar da hukunci kashe Al-mustapha da Shofolohan da alkali Mojilosa ya zantar a babban kotun jihar Legas a 30 ga watan Janairu, na shekara 2012.

An samu rahoton cewa, babban lauya jihar Legas kuma Kwamishinan Shari’a, Adeniji Kazeem, ya rattaba hannu akan takaddar daukaka karar “dakatad da hukuncin kotu zantarwa.”

Bayan shariar da ya dauki tsawon shekara goma sha biyu a kotun kolin jihar Legas, Mai shariar alkali Dada ya yanke wa Al-Mustapha da Sholahan hunkunci kisa a 30 ga watan Janairu na shekara 2012 saboda akawai hanun su a kisan Kudirat Abiola.

Mai sharia Amina Augie na kotun daukak kara a jihar Legas tayi watsi da hukuncin kashe Almustapha da Shofolahan saboda rashin kwakkawaran shaida a 12 ga watan Yuli na shekara 2012.

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.