Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Kara Sassauta Dokar Hana Fita

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Gwamnatin Jihar Kaduna, ta sassauta dokar hana fita tun daga ranar Laraba, da dare a cikin garin Kaduna, da kewayen sa nan take.

Samuel Aruwan, Kakakin Gwamnan Jihar ta Kaduna, Nasir El-Rufai, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce, daga yanzun mazauna garin na Kaduna, za su iya ci gaba da gudanar da harkokin su a kowace rana har ya zuwa karfe 10 na dare, da zuwa karfe 5 na safiya.

Talla

Sai dai, bayanan tsaro sun bayar da shawarar dokar hana fitan a garin Kachia, za ta ci gaba da kasancewa bayan karfe 5 na yammaci har ya zuwa karfe 6 na safiya, har sai abin da hali ya yi. Sanarwar na cewa, “A taron da hukumomin tsaro suka yi a yau, sun sake duba matsalar tsaro, sun kuma shawarci gwamnati da ta sassauta dokar hana fitan a wasu lokutan.

Wasu Abubuwan Masu Alaka

Hukumar Karota Ta Kama Mota Cike Da Tabar Wiwi

Talla
1 of 661

Kan haka, gwamnati ta amshi shawarar na su, inda ta dage lokacin da dokar za ta fara aiki har ya zuwa karfe 10 na dare.

Hakan ya zo ne saboda yanda abubuwa suka kara kyautatuwa a garin, domin sake farfado da harkokin neman abinci da al’umma ke yi a wannan lokutan na daren. Gwamnatin Jihar ta Kaduna ta yaba wa mazauna garin na Kaduna, kan yanda suka yi kokarin samar da zaman lafiya, ta kuma yi kira a gare su da su ci gaba da sanya ido sosai domin samar da dorewar zaman lafiyan.

Shugaba Buhari, ya yi alkawarin tabbatar da an fuskantar da wadanda suka haddasa rikicin a gaban shari’a, a sa’ilin da ya ziyarci garin na Kaduna, a ranar Talata.

 

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: