Gwamnatin jihar Kaduna na shirin fara sabuwar shari’a tsakaninta da shugaban ƙungiyar Harka Islamiyya a Najeriya, Ibrahim El-Zakzaky.
A ranar Laraba ne wata babbar kotu da ke zamanta a garin Kaduna ta wanke malamin da umurtar a sake shi tare da mai dakinsa Sayyada Zeenat.
Wata majiya a fadar gwamnatin jihar ta Kaduna ta ce ma’aikatar shari’a ta jihar na aiki kan shigar da karar a yanzu haka.
Sai dai a lokacin da muka tuntubi ɗaya daga cikin lauyoyi da ke kare malamin, Barista Sadau Garba, ya ce har yanzu ba su samu tabbaci game da rana ko lokacin da gwamnatin ke shirin fara sabuwar shari’ar ba.
Haka nan ma mai magana da yawun ƙungiyar ta Harka Islamiyya Ibrahim Musa ya ce suna ganin labarin ne kawai a jarida, amma har yanzu ba a tuntuɓe su game da sabuwar shari’ar.
Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matar tasa sun kwashe sama da shekara hudu a tsare tun bayan gurfanar da su a gaban kotu.
Add Comment