Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Sake Kaddamar Da Shirin Auren Marayu Karo Na Biyu A Masarautar Dutse

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Engr Magaji Abdullahi Mallammadori

Matar Gwamna Hajiya Asmau Muhammad Badaru Abubakar ita ce babbar baƙuwa a wajen Ɗaurin Auren, inda ta bawa amaren Gudunmawar na’urar ɗumama abinci da darduman Sallah (Sallaya).

Talla

Mai Martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi wanda shine Uban Taro yayi kira ga waɗanda suka ci moriyar shirin su mutunta aure kuma su zauna lafiya da mazajen su.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Ƙarƙashin shirin wanda gwamnatin Jihar Jigawa ta ɗauki nauyi, an zaƙulo marayu goma sha ɗaya daga kowace Ƙaramar Hukuma inda gwamnatin ta saya musu kayan ɗaki da suka haɗa da gado, katifa, filalluka, set na kujeru, madubi da sif na sa kaya wanda kuɗin su ya kai kimanin dubu ɗari uku da hamsin (₦350, 000).

Shugaban Kwamitin Aurar da Marayun wanda kuma shine mai bawa Maigirma Gwamnan Shawara akan Harkokin Addini da Masarautu, Malam Mujitafa Sale Kwalam yace an ɓullo da shirin ne domin taimakawa marayu da basu da gatan samun sayen kayan aure.

Ya ce shirin yana kan tafarkin addini ne wanda yayi kira da taimakawa marasa ƙarfi, kuma babu siyasa wajen zaɓan masu cimma moriyar shirin.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: