Gwamnatin Jahar Katsina Ta Gano Wajan Hakon Ma`adana Guda 442

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Falalu

Gwamnatin jihar Katsina Sun gano wajen tono Ma’adanai har guda 442 a cikin jihar, kanan, tuni sunfara shirye shirye kulla yarjejeniya yadda za’ a fara tonosu da wasu kamfanonin kamar yadda kwamishinan Ma’akatar Ma’adanai Alh.Mustapha Kanti Bello ya Sanar.

Ofishin yada labarai na gwamnatin Katsina wanda akafi sani da katsina media and publicity ta samu labarin wajen kwamishinan yayinda yake magana a wajen taron wayarma masu tono Ma’adanai kai karo na biyu da aka gudanar a jihar.yace ansamu wasu wajejen da za’ a Iya tono Ma’adanai a jihar don a halin yanzu har amba wasu kamfanoni damar fara aikin.

Yace yazama wajibi a dauki masu tono ma’adanai da muhimmanci yadda sana’ar Tasu zata kara samun karbuwa kuma yace wajibine a kirkiri wata kasuwa ta musamman a jihar yadda za’a rika saye da sayar da Ma’adanan.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 662

Yace babban gurin gwamnatinan shine fadada hanyoyin samun kudaden shiga kuma sashen tono ma’adanan kasa na daya daga cikin hanyoyin.

Gwamnatin ta kara kasafin kudinta a Ma’aikatar domin yin duk kan abinda yakamata.

Idan za’a tuna gwamnatin ta jihar Katsina a karkashin jagorancin Rt. Hon. Aminu Bello Masari tana daukar matakan samun kudaden shiga wanda ba na hanyar albarkatun Man fetur ba kawai gwamnatin na kokarin Jawo masu zuba jari domin samun kamfanoni a jihar, ta yadda za’a fadada hanyoyin samun kudin shiga, tareda samawa al’ummar jihar Ayyukanyi, da nufin rage zaman kashe wando musamman a tsakanin matasa.

Director General
Katsina Media & Publicity
Ibrahim M Abdullah
12th December 2018

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: