Gwamnatin Jahar Kano Zata Soke Yin Kayan Lefe Ko Taskira A Jahar ~Kwamishina Ta Fadawa Al’umma

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Gwamnatin jihar Kano zata duba yiwuwar soke kayan lefe da kayan daki a jihar a bikin aure, Kwamishiniyar harkokin mata Dakta Zahara’u Muhammad Umar ta bayyana hakan yayin tattaunawar ta da Jaridar Alkiblah a karshen mako.

Ta ce karya tayi yawa matuka a yanzu wajan aurer da yara, kuma Iyaye sune suke koyawa ‘ya’yansu kuma azo ana ta shan wahala karshe har ta kai ga an fasa auran domin an kure kowa.

Dakta Zahra’u ta bayyana cewa ba haramun bane ayi, amma yanda aka mayar dashi yanzu kowa yasani akwai yaudarar kai, kuma daman shi kwamishinan Addinai a jihar Dr Baba Impossible tini ya kyamaci wannan tsari na tarkacen kayan da yake wahalar da ma’auratan dama Iyayen su.

“Dan haka zamu zauna Insha Allahu da malamai da shi Baba Impossible mu fito da yanda za’a hana wannan karyar da ake yi”

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 906

“Kuma idan yara suna son junan su mu daura musu aure, idan taimako ya kama gwamnati ta bayar da abun da ya zama dole mai amfani” a cewar Dakta.

Dakta ta ce ko akwai masu hali da zasu iya yiwa ‘ya’yansu, amma wanda bazasu iya ba su suka fi yawa kuma suke takura kansu, bayan ko shi auran idan baka da hali Annabi Muhammad s.a.w cewa yayi a hakura ayi Azumi balle wani kayan daki ko lefe.

Sai kaga Amarya da Ango sun yi gwaram-gwaram da goshi duk sun zama kasusuwa sun lalace kafin aure.

Wannan jawabai sun biyo bayan fitowa da wata marubiciya kuma shugabar gidauniyar tallafawa marasa karfi Fauziyya D. Sulaiman tayi a ranar Juma’a tayi kira ga gwamnati, da malamai da Iyaye kan cewa akalli al’amarin lefe da kayan daki a sami masalaha domin ana iya aurar da ‘ya’ya mata batare da an shiga wani hali ba.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.