Labarai

Gwamnatin Iran za ta halatta auren dandano domin rage barna

Kasar Iran za ta shigo da auren mutu’a saboda yawan zinace-zinace

Bincike ya nuna cewa ana tafka mugun barna a Kasar musamman matasa

Auren dandano zai bada dama a rage fasikanci kafin ayi aure a Kasar

Mun samu labari daga Jaridar Daily Mail cewa ana kokarin kawo karshen kwanciya da maza kafin ayi aure a Kasar Iran.

 

Gwamnatin Kasar Iran za ta halatta auren dandano domin a rage barna a Kasar domin kuwa bincike ya nuna kashi 80% na ‘Yan matan kasar kan kwanta da wani kafin su yi aure.

Kusan daya cikin biyar kuma na wannan kason kan bi ‘Yan uwan su ne mata.

Auren dandano kan bada dama mutum ya sadu da wata na dan lokacin kafin a rabu.

Wannan zai yi maganin zinace-zinacen da ake tafkawa a Kasar.

Gidan labarai na Fox News yace tun yara mata su na kanana ake fara kwanciya da su. Mafi yawan mutanen kasar dai yara ne matasa.

Kwanaki kun ji cewa rashin Maza na aure a Najeriya na nema ya zama wani tashin hankali.

Mazan aure su na matukar wahala a halin yanzu saboda jiran mai kudi.

 

Souce In Naija.com

 

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.