Majalisar zartaswa ta jihar Bauchi ta amince da canja sunan Jami’a Mallakar jihar Bauchi daga Bauchi State University Gadau zuwa Saadu Zungur University.
Kwaminshinan ilimi na jiha Dakta Aliyu Tilde ne ya bayyana hakan inda ya kara da cewa nan gaba kadan za’a fara bikin sauyin sunan.
A cewar Dakta Tilde gwamnati ta nazarci gwagwarmaya da saudakar da kai wajen bautawa Kasa da horo bisa neman ilimi da Marigayi Mallam Saadu Zungur wanda Dan asalin jihar Bauchi yayi tsawon rayuwarsa.
Shaharraren malamin makaranta, masanin lugga da adabi kuma Dan rajin kare hakkin Dan Adam da gwagwarmayar siyasa, Mallam Saadu Zungur wanda ya rayu tsakanin shekarun 1915-1958 ya taba rike Sakataren NCNC.
Tilde yace matakin na cikin shirin Gwamna Bala Muhammad na karrama yan mazan jiya da suka yi fice wajen tallafawa al’umar jiha da ma kasa baki daya.
Wannan rana a cewar kwamishinan na ilimi abar farin ciki ce ga Gwamna Bala Muhammad, gwamnatinsa da ma al’umar jihar Bauchi.
Lawal Muazu Bauchi
Me tallafawa Gwamna Bala Muhammad kan kafafen yada labarai na zamani
Laraba,10,Febrairu 2021