Labarai

Gwamnati Ta Mika Tafiyar Da Filayen Jiragen Saman Abuja Da Lagos Ga ‘Yan Kasuwa

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya tabbatar da cewa majalisar ministoci ta amince da mika tafiyar da harkokin filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Lagos da kuma filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ga ‘yan kasuwa.

Tun a shekarar da ta gabata ne, gwamnati ta bayyana shirinta na mika manyan filayen saukar jiragen sama ga ‘yan kasuwa don inganta su, lamarin da ya fusata ma’aikatan filayen jiragen wadanda suka yi alwashin bin duk matakin da ya dace na ganin wannan shiri bai samun nasara ba.

 

Rariya

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.