Daga Comr Abba Sani Pantami
Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu, ya bada wa’adin mako daya ga makiyaya su bar kungurumin jejin da ke cikin jiharsa.
Gwamnan ya bada wannan wa’adi ne a yankurin da yake yi na kawo karshen matsalar garkuwa da mutane da sauran ta’adin da ake yi a jihar.
Sanarwar Rotimi Akeredolu ta fito ne kai tsaye a shafinsa na Twitter, a ranar Litinin 18 ga watan Junairu. 2021.