Gwamnan Katsina ya bawa Rarara da Baban Chinedu Kyautar miliyan 80 da sabon gida
Biyo bayan hare-haren da aka kai gidan fitattun mawakan siyasa biyu a ranar 20 ga watan Maris da wasu ‘yan daba suka kaddamar a jihar Kano a lokacin zaben gwamnan jihar da aka gudanar a kwanakin baya, Gwamna Masari na jihar Katsina ya amince tare da bayar da kyautar Naira miliyan 80 ga mawakan jam’iyyar(APC) guda biyu.
Wannan karimcin wanda ya zo kasa da mako guda a mika wa sabuwar gwamnati, an yi nufin Dauda Adamu Rarara da Yusuf Baban Chinedu a kokarin tallafawa jam’iyyar.
Majiya Channelstv
Add Comment