-Advertisement-


Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje Ya Kaddamar Da Gidajen Rugar Fulani


0 222

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya kaddamar da gidajen Rugar Fulani a dajin Dansoshiya dake karamar hukumar Kiru wanda Gwamnatin sa ta samar domin samarwa makiyaya matsuguni domin kiwo a waje daya mai maimakon yawo da suke.

Rugar wadda zaa gina gidaje 200 a nan gaba, an fara ne da gidaje 25 a yanzu wanda Gwamna Ganduje ya kaddamar kuma ya bawa fulani a kyauta, sannan akwai rijiyar burtsatse ta zamani mai aiki da hasken rana wato solar guda biyar, sannan a nan gaba zaa samar da makaranta, asibiti, ofishin yansanda da kuma katoton dam na ruwa domin shayar da shanun su.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 608

-Advertisement-

Gwamna Ganduje na tare da mataimakin sa Dr Nasiru Yusuf Gawuna da Kwamishinan ruwa Hon Sadiq Wali da sauran manyan jami’an Gwamnati.

Salihu Tanko Yakasai

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.