Labarai

Gwamnan Jihar Neja Ya Ɗauki Nauyin Iyalan Jami’an Tsaro Da Suka Rasa Ransu A Bakin Daga

Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya yaba da ƙoƙarin jami’an tsaron haɗin gwiwa da ke aiki a ƙauyen Kundu, dake ƙaramar hukumar Rafi bisa yadda suka daƙile harin da ƴan bindiga suka kai ƙauyen wanda ya sanadin mutuwar da dama daga cikin ƴan ta’addan da jami’an tsaro biyu.

Gwamna Sani Bello ya yi wannan yabo ne lokacin da ya ziyarci sansanin jami’an tsaron da ke ƙauyen Kundu domin jajantawa jami’an tsaron da kuma ƙara musu ƙwarin gwiwa, tare da alƙawarin sake duba yanayin tsaro a yankin domin inganta shi.
Gwamnan ya ce ya gamsu da martanin da jami’an tsaron suka yi wa ƴan ta’addan sannan ya yi alƙawarin tallafa wa iyalan jami’an tsaron da aka kashe, yana mai cewa jihar ta samu zaman lafiya a ƴan kwanakin nan.

Ya kuma yarda cewa babu inda babu matsalar tsaro, yana mai bayar da tabbacin cewa gwamnatin sa zata yi iya ƙoƙarinta don rage matsalar rashin tsaro zuwa mafi ƙarancin tsaro.

“Babu wani wuri da yake da tsaro dari bisa dari amma za mu yi duk abin da ya kamata don dawo da zaman lafiya. Muna kashe kuɗi wurin sayen kayayyakin yaƙi da matsalar tsaro da sauran kayan aiki don taimakawa wajen yakin da kuma rage asarar rayuka,” in ji shi.

Gwamnan ya yi ganawar sirri da shugabannin hukumomin tsaro waɗanda suna daga cikin tawagarsa, kwamandan sansanin da sauran masu ruwa da tsaki don samun ƙarin haske game da daƙile harin da kuma bayar da shawarwarin hanyoyin ci gaba.

Wasu daga cikin mazauna ƙauyukan wadanda suka ba da labarin yadda harin ya kasance sun yaba wa jami’an tsaron na haɗin gwiwar bisa yadda suka sha ƙarfin ƴan bindigar da suka bayyana cewa abin da jami’an tsaron suka nuna ya ba su ƙwarin gwiwar ci gaba da zama a ƙauyen.

An bayyana cewa, ƴan bindigar da yawansu ya zarce 100, sun kai farmaki sansanin jami’an tsaron da misalin ƙarfe 9 na safe, inda suka yi musayar wuta da jami’an tsaron nabtsawon awanni biyu amma ba su yi nasara ba, inda aka ce da dama daga cikin ƴan ta’addan basu ji ta dadi ba a hannun jami’an tsaron domin bayaga waɗanda aka kashe, da dama daga cikin su sun tafi da munanan raunuka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: