Labarai

Gwamna Tambuwal Ya Kaddamar Da Bude Sabon Gidan Gwamnatin Bauchi

Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP kuma gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranci takwarorinsa gwamnonin PDP wajen bikin bude sabon gidan gwamnatin jihar Bauchi.

Da yake jawabi yayin bikin, Gwamna Tambuwal yace la shakka aikin zai amfani al’uma da gwamnatin jihar Bauchi kana yayi amfani da damar wajen yabawa gwamna Bala Muhammad kan aikin.

Tambuwal Waziri yace zauren gwamnonin PDPn yayi imani da samar da sauyi wa al’umar Najeriya a saboda haka ne ma suka dukufa wajen kammala ayyukan da gwamnatocin baya suka yi watsi da su a jihohin su don ciyar da Najeriya gaba.

Ya kara da cewa jam’iyyar PDP a kullum burin ta samar da ayyukan cigaba da za su tallafawa rayuwar al’umar Najeriya.

Shima a nasa jawabin, Gwamna Bala Muhammad cewa yayi aikin fadada da sabunta gidan gwamnatin na cikin shirin gwamnatin sa na inganta birane da yankunan karkara.

Tun farko da yake jawabi, Sakataren gwamnatin jiha Barrister Ibrahim Kashim yabawa gwamna Bala yayi kan hangen nesa da canja tarihin jihar Bauchi ta hanyar ayyukan raya kasa.

Tawagar gwamnonin jam’iyyar PDP, jami’an gwamnati da manyan baki sun shaida bude sabon gidan gwamnatin.

Lawal Muazu Bauchi
Me tallafawa Gwamna Bala Muhammad kan kafafen yada labarai na zamani
26/21/07

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: