Labarai

Gwamna Katsina ya amince da nadin Abdullahi Aliyu Yar’adua a matsa yin Darakta na Hukumar Kula da Dakin Karatun Jiha watau (Katsina State Library Board) a turance.

Gwamna Aminu Bello Masari ya amince da nadin Alhaji Abdullahi Aliyu Yar’adua a matsa yin Babban Darakta na Hukumar Kula da Dakin Karatu ta Jiha watau (Katsina State Library Board) a turance.

 

Kafin nadin nashi, Alhaji Abdullahi Yaradua shi ne Babban Sakataren yada labarai na ofishin Sakataren Gwamnatin jiha kuma gogaggen ma’aikaci ne a gwamnatin jiha.

 

Wanda ya fara da aikin koyarwa, daga bisani ya koma Gidan Rediyon Jiha inda ya hau matakai daban daban har ya kai matsayin Darakta.

 

Alhaji Abdullahi Aliyu Yaradua ya sami Digirin shi na farko a Jami’ar Al-Qalam dake nan Katsina a fannin Turanci.

 

Haka kuma Digirin shi na biyu ya yi shi a fannin Adabin Turanci (English Literature) amma a jami’ar Bayero dake Kano. Yanzu haka kuma yana karatun Digirin Digirgir (PhD) a jami’ar ta Al-Qalam.

 

Muna mashi addu’a da fatar Allah Shi mashi jagora.