Labarai

Gwamna Inuwa Ya Kaddamar Da Allurar Rigakafin Cutar Corona A Jihar Gombe

Daga Haji Shehu

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya kaddamar da allurar rigakafin cutar Korona a hukumance a jihar.

Likitan gwamnan Dakta Bello Abdulkadir ne ya yiwa gwamnan Allurar ta kamfanin AstraZeneca a babban dakin taron gidan Gwamnatin jihar Gombe.

Da yake jawabi jim kadan bayan an yi masa allurar, Gwamnan ya ce samarda allurar rigakafin na Covid-19 alamu ne dake nuni da al’amura zasu daidaitu a hankali.

Gwamnan ya kara da cewar, zuwan rigakafin zai kawo karshen tarnakin da cutar ta yiwa harkar sufuri da kuma aiki.

Inuwa ya bukaci masu rike da mukaman siyasa, shugabannin addini da na gargajiya da su goyi bayan aiwatar da allurar rigakafin ta Covid-19 a duk fadin kananan hukumomin jihar.

Jihar Gombe ta karbi jimilar allurai 71,340 daga Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Bunkasa Kiwon Lafiya a Matakin Farko.

Gwamna Inuwa ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bada muhimmanci ga lafiyar ‘yan kasar, yana mai cewa a matsayinsa na Gwamnan jihar alhaki ne akansa ya tabbatar da lafiyar jama’a da jin dadinsu da kuma basu kulawa yadda ake bukata.

RAHOTON INUWA 4+4 TV

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: