Labarai

Gwamna Ganduje ya sake jaddada kudurin hadin kan kasa

-Gwamnan jihar Kano ya sake nanata kudurin hadin kan kasar Najeriya

– Ganduje ya karbi bakoncin wakilan ‘yan kabilar Igbo na jihohin arewa 19 a lokacin da suka ziyarce shi

– Gwamnan ya ce duk ‘yan Najeriya na da incin zama a duk bangarori na kasar

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, ya nanata cewa gwamnatinsa ta sadaukar da hadin kan kasa, yayin da kuma ya nace cewa ‘yan kabilar Igbo mazauna a fadin jihar ba za su bar jihar ba.

Ganduje ya yi wannan alwashin ne a lokacin da wasu wakilan ‘yan kabilar Igbo na jihohin arewa 19 suka kai masa ziyara a gidan gwamnati da ke Kano.

Arewablog ta ruwaito cewa wannan kalaman gwamnan na da halaka da wa’adin ficewa daga arewa da shugabanin kungiyoyin matasan arewa suka ba ‘yan kabilar Igbo.

Ganduje ya ce: “Ba za mu ƙyale, ku tafi ba, kana babu inda saku kuma babu inda zaku tafi domin Kano gida ne gare ku”.

 

Gwamnan ya ce duk ‘yan Najeriya na da incin zama a duk bangarori na kasar ba tare da banbancin addini ko kabilanci ba.

Gwamnan ya ce Igbo mazauna a jihar sun kasance ‘yan asalin Kano, kamar kowane dan Najeriya mazaunin a Kano zai ci gaba da zama’ yan asalin jihar.