Gwamna Ganduje Ya Bayyana Abinda Zai Faru Da PDP Idan Har Ta Kai Kararsa Gaban Kotu


0 269

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Zababben gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya nuna ma jam’iyyar PDP yatsa, tare da gargadinta game da abinda zai biyo baya idan har ta garzaya gaban kotu akan kalubalantar nasarar daya samu a zaben daya gudana makonni biyu da suka gabata.

Majiyarmu ta ruwaito Ganduje yace jam’iyyar PDP za tayi da-na-sanin kalubalantar nasararsa data shirya yi a gaban kotu, haka nan kuma wannan matakin da suke shirin dauka zai tarwatsa jam’iyyar kanta.

Ganduje ya bayyana haka ne yayin daya karbi bakuncin dubun dubatar masoya da magoya baya da suka fito kai masa ziyara daga garin Ganduje, cikin karamar hukumar Dawakin Tofa a ranar Litinin, 1 ga watan Afrilu.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da kwamishinan watsa labaru na jahar Kano, Muhammad Garba ya fitar, inda yace cewa “Kafin zaben makon daya gabata da muka yi nasara, PDP ta yi amfani da magudin zabe iri iri wanda daga bisani muka bankadosu.

“Amma daga bisani da aka yi zaben gaskiya da gaskiya, kuma aka hana su damar yin magudi, ai kaga sahihan sakamakon da zabukan suka nuna, don haka nake ganin suna gab da daukan matakin da zai lalatasu gaba daya, kaikayi zai koma kan mashekiya.

“ Abdullahi Umar Ganduje.

#Mikiya

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.