-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Gwamna El-rufai Ya Jagoranci Tattakin Nuna Muhimmancin Zaman Lafiya A Yayin Zabe


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Gwamna Malam Nasir Ahmed El-Rufai ya jagoranci wani tattaki na musamman da matasan Jam’iyyar APC na Jihar Kaduna suka shirya domin nuna muhimmancin zaman lafiya a Jihar Kaduna a zabe mai zuwa.

An shirya wannan tattakin ne karkashin jagorancin Hajiya Maryam Abubakar, Mataimakiya ta Musamman ga gwamnan a kan shafukan sada zumunta.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 659

- Advertisement -

Hajiya Maryam a zantawar da ta yi da manema labarai ta bayyana cewa manufar wannan tattaki shi ne domin a nuna wa matasa muhimmancin zaman lafiya a rayuwar al’umma saboda zabe ba yaki ba ne, hanya ce kawai ta samar da shugabanni a demokradiyyance.

Wadannan matasa karkashin jagorancin Gwamna El-Rufai haka suka bi hanya suna rarraba takardu masu dauke da maganganu na jawo hankalin jama’a kowa ya zabi wanda yake so ba tare da wata tsangwama ba.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: