Labarai

Gwamna El-Rufai Ya Gana Da Shugabannin Al’umma

Gwamna El-Rufai yau Laraba ya gana da shugabannin addinai da shugabannin gargajiya a wani taro da Hukumar Kasa da Safiyo ta shirya a dakin taro da ke Murtala Square Kaduna.

Gwaman ya nemi shugabannin al’umma da suka hada da limamai da fastoci da masu unguwanni da su taimaki al’umma, su kuma taimaki gwamnati wurin ganin an wayar da kan al’umma bisa kyawawan manufofin gwamnati da take da shi na ganin ta kawo wa al’umma cigaba musamman kudirin da gwamnati take da shi na fadada garin Kaduna ta fuskar arewa da yamma.

Malam Nasir El-Rufai ya bayyana wa wadannan iyayen kasa cewa, Hukumar Kasa da Safiyo ta shirya wannan taro ne saboda Gwamnatin Jihar Kaduna garin Kaduna ta cika kuma gwamnati ta shirya fadada garin ta shiyyar arewa da yamma wanda ya fado cikin kananan hukumomin Igabi da Chikun.

El-Rufai ya jawabinsa ya nemi iyayen kasa da su tsaya tsayin daka wurin yin gaskiya musamman wurin bayar da shedar mallakar filaye saboda gwamnati ba ta sanya hannu a kowace takardar mallakar fili sai da sa hannun dakace ko mai unguwa ko hakimi musamman a wannan lokaci da gwamnati za ta karbi filayen ta biya diyya domin a samu a fadada garin Kaduna.

A jawabin nasa, Gwamnan ya nemi al’umma su kara bayar da goyon baya ga Gwamnatin Jihar Kaduna a kokarin da take yi na fadada garin na Kaduna domin hakan shi zai kawo masana’antu su shigo jihar wanda hakan zai samar da dimbin ayyukan yi ga matasa. Ya bayar da misalin irin arzikin da Kamfanin Olam ya kawo wa jihar wanda duk shekara kawai yana siyan masara sama da buhu miliyan dari da hamsin daga manoman jihar Kaduna.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: