Gwamna Bauchi Ya Gwangwaje Kananan Hukumomin Jihar Bauchi Da Na`urar Tiransifoma Sama Da Sittin

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Mohammed A. Abubakar, ta kaddamar da rabon na’urar samar da wutan lantarki na (Transformer) har sama da guda sittin, mai karfin kba 500 ga kananan hukumomin jihar guda 21.

An kaddamar da rabon ne a sakateriyar gwamnatin jihar Bauchi.

Talla

Gwamna M.A ya shaidawa Shugabannin kananan hukumomin jihar Bauchi cewa alhakin sayan na’urar samar da wutar lantarki ba yana kan gwamnati bane, ya yi hakan ne domin cire talakawan jihar daga matsalolin wutar lantarki da suke fama da shi.

Gwamnan ya kuma ja kunnen shugabannin kananan hukumomin da su kula da na’urorin dan gudun barnatawar.

Wasu Abubuwan Masu Alaka

Sheikh Dahiru Bauchi Ya Yaba Wa Gwamna Mai Mala Kan Inganta…

Talla
1 of 661

Shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi na jihar Bauchi (ALGON) Shugaban karamar hukumar Katagum ya yi godiya ga Gwamna M.A kan irin wannan kulawa da talakawa da gwamnatinsa me yi, ya sha alwashin kulawa da wadannan na’urar da gwamnatin ta samar musu da shi. Ya ce za su tabbatar da cewa jama’ar su sun amfana da na’urar ta inda ya da ce.

Mai tallafawa gwamnan jihar Bauchi kan Sadarwa, Shamsuddeen Lukman Abubakar, ya bayyana cewa kowace karamar hukuma za ta samu nauran bada wutar guda uku ne cikin dukkanin kananan hukumomin jihar Bauchi..

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: