Labarai

Gwamna Bala Ya Ginawa Almajirai Kayatacciyar Makarabtar Zamani A Jihar Bauchi

Wannan makaranta da kuke gani cikin hotuna makaranta ce ta Almajirai da Kauran Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya sake mata gyara tare da sake wasu gine gine bayan da tsohuwar gwamnatin kayayyen gwamna M.A ta watsar da makarantar tare da wofintar da duk wani sha’ani na makarantar.

Makarantar ta kunshi.

Ajujuwan Almajirai
Wajen Kwanan Almajirai
Wajen Cin Abincin Almajirai..
Ban Ďakunansu..
Ofishin Malamai..
Wajen kwanan malamai….
Wajen Diban ruwa (Boreholes) da sauransu.

Akwai abubuwa da ba’a kammala aikinsu ba, kamar Masallaci, sanya Transfomer, da zai bada hasken lantarki, gadajen dalibai, wanda tuni mai girma Gwamna Bala Muhammad Kauran Bauchi yayi alkawarin karasawa jim kadan bayan da yazo ziyarar gani da ido a yammacin jiya Litinin 1 ga Maris, 2021.

Wannan makaranta dai Gwamna tuni ya miqata wa Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi domin cigaba da assasa tare da koyawa yare addinin islama a ciki.

Allah ya sakawa Jonathan da alkairi wanda shine ya kafa tubalin gina wannan makaranta ya kuma sakawa mai girma gwamna Kauran Bauchi da alkairi da ya sake dawo da ita.

Yusuf Adamu Abdullahi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: