Labarai

Gwamna Bala Ya Ceto Rayuwar Yarinyar Da Matsafa Suka Yanka Al’aurarta

Idan za ku tuna kwanaki ne Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya dauki nauyin ceto wata yar shekara shida bayan da matsafa suka yanke mata sashin al’auranta al’amarin da ya sanya Gwamnan kuka bisa tausayawa nan take kuma ya biya mata kudin magani da aikin da akayi mata gaba daya.

Alhamdulillahi likitoci sun yi nasarar yi mata aiki cikin al’aurar ta yanda suka yi mata tiyata domin ceto rayuwarta.

Lamarin dai ya faru ne a karamar hukumar Jama’are inda yarinya ta faɗa hannun matsafa inda suka illata gabanta wajen yin wani ƙulumboto na su na tsafi.

Cikin taimakon Allah gwamnan jihar Bauchi ya ya sa a gaggauta kaita asibiti inda ka yi mata nasaran mata aiki mai inganci a gabanta kuma yanzu komai ya dawo daidai. Kamar yadda iyayen yarinyar suka sheda ma wakilin LDB.

Iyayen yarinyar sunce mai girma Gwamnan jihar Bauchi ya tsaya kan maganar ya tabbatar ta samu lafiya hakan ya tabbatar mu Gwamnan mutum ne na jama’a dake da ruhi na imani da tausayi a tattare da shi. Sunyi masa addu’ar Ubangiji Allah ya kare shi ya tabbatar da alheri cikin mulkin sa.

𝘋𝘢𝘨𝘢 𝘖𝘧𝘪𝘴𝘩𝘪𝘯 𝘮𝘢𝘪 𝘵𝘢𝘭𝘭𝘢𝘧𝘢𝘸𝘢 𝘎𝘸𝘢𝘮𝘯𝘢𝘯 𝘫𝘪𝘩𝘢𝘳 𝘉𝘢𝘶𝘤𝘩𝘪 𝘬𝘢𝘯 𝘚𝘢𝘣𝘣𝘪𝘯 𝘬𝘢𝘧𝘰𝘧𝘪𝘯 𝘺𝘢𝘥𝘢 𝘭𝘢𝘣𝘢𝘳𝘢𝘪*
𝘓𝘢𝘸𝘢𝘭 𝘔𝘶𝘢𝘻𝘶 𝘉𝘢𝘶𝘤𝘩𝘪

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: