Ya bayyana hakan ne ta cikin shirin rediyo Jigawa mai suna Mai Damarar Aiki. Inda Alhaji Ya’u Mai Unguwa Jaga, Shugabannin Hadaddiyar kungiyar manoma ta kasa reshen jihar Jigawa (AFAN) ya bayyana cewa gwamnatin jihar jigawa zata cirri tuta wajen habaka bangaren aiyukan gona a kasar nan.
Shugaban kungiyan yace gwamnatin jiha tayi fice wajen tallafawa bangaren aikin gona ta hanyar samarwa manoma ingantaccen iri, da taki, da kuma magungunan kwari.
Yace gwamna Badaru Abubakar ya ba ma shirin noma dan riba muhimmancin da ya dace domin kuwa an samar da hecta 50 a kowace mazaba domin gwajin noma dan riba wanda aka bada iri, da taki bashi da kowane manomi zai biya bayan girbi.
Yace gwamnan jihar ya damu da harkar noma wanda hakan ke nuni da cewa nan bada jimawa ba jihar Jigawa zata iya noma abinchin da zai iya ciyar da kasar nan da ma afirka baki daya
Shugaba Ya’u ya bada misalin cewa bullo da shirin noman Dangote a jihar Jigawa ya sanya wani manomi daya tak ya samu bahu 120 a hecta guda na shinkafa.
Shugaban na AFAN ya kuma danganta nasarorin da aka samu a fannin gona a jihar Jigawa akan JARDA da JASCO bisa samar da malaman gona, ingantacceen iri, da maganin kwari, da kuma taki.
Ya bayyana cewa tsarin noma dan riba da aka kirkiro a jihar ya samarwa dinbin matasa aiyukan yi.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar a matsayin gwamnati ce mai san cigaban al-ummah.
Alhaji Mai Unguwa Jaga ya kara da cewar manoman Jigawa 100 zasu halarci bikin nunin iri da za a gudanar a Birnin Abuja da zasu nuna irin shinkafa, da dawa, da alkama, da sobo, da waken suya, da kuma kankama.
Daya juya ga kungiyar ta AFAN kuwa shugaba Jaga yace an kafa kungiyar ne domin samarwa manoma ingantaccen iri daga gwamnatocin tarayya da jihohi inda daga bisani aka hada kungiyar da majalissar kula da ingantaccen iri ta kasa domin ba ma manoma iri ta hannun kungiyar.
Alhaji Ya’u Jaga yace suna da rassa a kowace kananan hukumomi da mazabu da nufin isar da sakonnin kungiyar ga manoma domin cigaban aiyukan gona.
Ya kuma bada shawara akan ba ma manoma bashi ta hanyar kungiyar domin biyan bashin akan lokaci.
Ga hoton Gwamna Badaru Abubakar da Alh. Dangote lokacin da aka kaddamar da noman shinkafan Dangote a shekaran da ya gabata.


Ga hotunan gwamnan da manona a gonayen su.




Add Comment