A wata budaddiyar wasika zuwa ga gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, sakataren Kungiyar Inuwar Mutanen Bida ya zargi gwamnatin jihar Neja da nuna halin ko in kula da makarantar koyon aikin jinya da ke Bida a jihar ta Neja, hukuncin da a cewar sakataren na kungiyar mutanen Bida ya haifar da sanya makarantar durkusawa a kan gwiwoyinta
Ya ci gaba da cewa aikin farfado da makarantar zai ci kudi akalla wuri na gugan wuri Naira milyan 350 ta yadda makarantar za ta samar da kayayyakin koyo da koyarwa da makarantar ke da bukata, gina azuzuwan daukan darasi da ofisoshin malamai, da dakunan gwaje-gwaje da sauransu, tare Kuma da daukan ma’aikata ta yadda makarantar za ta tsallake siradin tantancewar cika sharuddan horas da daliban aikin jinya da ungozoma da za a gudanar akanta a kwanannan.

Sai dai abin takaicin shi ne yadda gwamnatin jihar Neja bisa jagorancin Abubakar Sani Bello ta ware wa makarantar Naira miliyan 15 kacal a kasafin kudin 2016, a inda a daya hannun Kuma gwamnati ta ware wasu kudade sama da abinda za a kasha don farfado da Makarantar Koyon Aikin Jinya Ta Bida don kafa wata sabuwar makarantar koyon aikin jinyar a mahaifar gwamna wato Kontagora.
Sakataren na Inuwar Mutanen Bida ya yi kira ga gwamnan da ya farfado da Makarantar Koyon Aikin Jinya da ke Bida da a halin yanzu ke a halin gargara. Ya ci gaba da cewa, kudaden da gwamnati ta ware don kafa sabuwar makarantar koyon aikin jinya a Kontogora ya isa ya gyara makarantar bida tare da dawo mata da ruhinta ta yadda za ta yi kafada da kafada da sauran takwarorinta a fadin Nijeriya.
Kwalejin Kimiyyar Aikin Jinya Ta Bida wacce a baya ake kira da Makaranatar Koyon Aikin Jinya Ta Bida akafa ta ne a shekarar 1976 da niyyar samar wa jihar ta Neja da ma’aikatan aikin jinya don cimma kudirin jihar na samar da ingantacciyar lafiya ga daukacin al’ummar jihar da mafi akasarinsu mutanen karkara ne.
Ga budaddiyar wasikar da sakaran Dyadya ya rubuta ga gwamna da harshen Ingilishi.

Add Comment