-Advertisement-


Gwamna Abdullahi Umar Ganduje Ya Tsige Kwamishinan Ayyuka Bisa Kalaman Batanci


0 697

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

GANDUJE YA TSIGE KWAMISHINAN SA NA AIYUKA MU’AZU MAGAJI SABO DA YAYI KALAMAN BATANCI GA ABBA KYARI JIM KADAN BAYAN MUTUWAR SA.

@faizualfindiki

Gwamnatin jihar Kano, Karkashin Jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje Khadimul Islam, ya sauke nadin kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa, Engr. Muazu Magaji ga sakamako nan take.

An cire kwamishinan ne bayan kalaman sa marasa dadi da ya yi a kan marigayi Shugaban Ma’aikatan fadar Shugaban Kasa, Malam Abba Kyari. kuma hakan ya sabawa doka kuma hakan zubarwa da Gwamnati mutunci ne a bayyane.

A matsayin sa na ma’aikacin gwamnati, kwamishinan yakamata ya maida hankali akan ayyukan ofis din sa ta hanyar nisantar duk wani aiki da zai iya zubar da mutuncin ofishin amma hakan yaci tura.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 608

-Advertisement-

Jama’a dadama sun jima sunata kira ga gwamna akan ya taimaka ya cire wannan Kwamishinan jim kadan bayan mutuwar abba kyari. Inda muma mukai ta kira ga gwamna akan yaja masa kunne akan irin wayannan abubuwan da yakeyi marasa kan gado.

Ayyukan ma’aikacin gwamnati, na gwamnati ne, akasin hakan ya nuna baya ga gwamnati ne saboda haka, gwamnatin Ganduje ba za ta lamunci mutanen da suke shiga cikin harkar sayar da kai ko akasin haka ba don fakewa da ita azubar mata da mutunci.

Kowa yasan marigayi Abba Kyari ya yi rayuwa wacce ta cancanci abin koyi ta hanyar bauta wa kasarsa gwargwadon iyawarsa.

Allah ya jikan Malam Abba kyari Allah yasa Aljannace Makomar sa Amin.

Faizu Alfindiki
S.A. Public Affairs
Kano State Government House.
18th, April, 2020.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.