Labarai

An gurfanar da wani malamin Islamiyya kan zargin yin lalata da wasu yan mata Uku

Iyayen wasu yan mata uku ‘yan shekara 7 zuwa 12 sun kai karan malamin dake koya wa ‘ya’yansu karatun Arabi kotun dake Ikeja saboda aikata lalata da yake ta yi da yaran su uku tun daga watan Mayu zuwa Agustan wannan shekara.

Clifford Ogu wanda ya shigar da karan ya ce malamin da ke zama a No. 2, Kelani St., Adealu Bus Stop in Dopemu, kusa da Legas na lalata da yaran a gidansa a lokacin da suke zuwa karatun Arabin.

Ya ce iyayen yaran sun sami labarin abin da malamin ke wa yaran su ne a lokacin da suke neman sabon malamin domin sun canza wurin zama.

“Karaman cikin su ta fada wa mahaifiyar su cewa basa bukata a canza musu malami. Da mahaifiyarsu ta nemi ta sani ko menene dalilin hakan shine ‘yar ta fada mata abin da malamin ke yi musu idan sun je karatu.”

Nan da nan mahaifiya tare da Cliford Ogu suka kai karan malamin ofishin ‘yan sanda.

Malamin ya karyata zargin da iyayen yaran suka yi mishi.

Alkalin kotun Taiwo Akanni ya bada belin malamin kan Naira 250,000 tare da shaidu biyu wanda malamin zai kawo sannan ya daga shari’ar zuwa 11 ga watan Satumba.

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.