Nasiha

Gudunmawar Da Za Mu Bayar, Domin Samun Saukin Watan Ramadan

Daga Bashar Mustapha Bashar
A wannan lokaci da azumin watan Ramadan ke ƙara towa, kowa nada Irin tashi gudunmawa da zai iya bayarwa domin saukaka ma al’ummar Musulmi musanman masu ƙaramin karfi domin samun rahamar Allah SWT acikin watan Ramadan.

Misali:
✔️ Gwamnati…za ta iya taimakawa ta hanyar rage haraji ga kamfanoni da zinmar su ragewa kayayyaki da suke samarwa kuɗi don masu karamin ƙarfi, su samu sukunin gudanar da azumi da bukukuwan Sallah cikin sauqi da samun Sa’ida.

✔️ Kamfanoni, suma sukan Iya yin tasu hubbasar ta hanyar rage farashin kayan da suke samarwa tareda Sa’ido ga ƙananan yan kasuwa da zinmar suma su rage nasu farashin Kamar yadda suka umurta, kamar yadda yake gudana awasu kasashen larabawa.

✔️ ‘Yan kasuwa, a nan ina nufin ‘yan kasuwa masu hulda da jama’a kai tsaye manya da kanana suma sukan iya bada tasu gagarumar gudummawa ta hanyar jin tsoron Allah akan su daina tsauwalawa kaya kudi koma boyesu da niyyar yin kuɗi da watan Ramadan, su sani cewa Allah shike arzirtawa ba tsadar kayayyaki ba.

✔️ Masu Dukiya, a nan ina nufin duk wanda Allah Ya huwa cewa abinda zai taimaki wani, Yayi kokari Yayi haka saboda fadin Ma’aiki SAW duk wanda ya budawa mai azumi baki Allah SWT zai saka masa da aljanna Firdausi.

✔️Daga karshe PHCN ko NEPA, Yakamata ku sani cewa wutar lantarki musanman a irin wannan lokaci na watan Ramadan tanada matuqar anfani ga jama’a saboda samun ƙanƙara da kuma gudanar da aikace aikace kamar anfani da ita wurin IBADODI Kamar Salloli, karatun Alkur’ani, Tafsir da ɗinke ɗinke saboda bukukuwan Sallah.

Da fatan Allah Ubangiji Ya baiwa kowa ikon sauke nauyin daya rataya akansa kuma ya nuna mana, muna fatan fara azumi lafiya mu kuma kammala lafiya. Amin

Bashar M Bashar ✍️✍✍️
Chairman “Arewa Media Writers”,
Reshen Jihar Sokoto.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement