Labarai

Gobara Ta Tashi A Gidan Da Ganduje Zai Koma Idan Ya Sauka Daga Mulki

Gobara Ta Tashi A Gidan Da Ganduje Zai Koma Idan Ya Sauka Daga Mulki

 

Gobara ta tashi a gidan da gwamnan jihar Kano mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje, zai koma idan ya kammala mulki.

 

SOLACEBASE ta rawaito cewa gidan na kan titin Miagun, bayan Kano Club, a unguwar Nasarawa GRA.

 

Gobarar dai ta tashi ne da yammacin ranar Litinin, in da ta kone kaya na miliyoyin Naira.

 

Jaridar ta ce majiya mai tushe ta shaida mata cewa, gobarar ta kone sashin da ake kiwon shanu da sauran dabbobi kuma da yawa daga cikin dabbobin sun mutu.

 

Da aka tuntubi babban sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar, ya ce ba ya gari, don haka ba shi da masaniyar faruwar lamarin

 

Sai dai jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf, ya tabbatar da tashin gobarar.

 

Ya kuma ce an shawo kanta a lokacin da jami’ansu suka isa gidan.