GGSS JANGEBE: Ƴan Bindiga Sun Sace Dalibai Mata Kusan 300 A Jihar Zamfara

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Suleiman Abba (TBABA)

A jihar Zamfara ‘yan bindiga sun sace ɗalibai mata fiye da 300 daga makarantar sakandiren GGSS Jangeɓe da ke jihar ranar Alhamis da daddare.

Mahaifin daya daga cikin daliban da kuma wani malami da ke makarantar lokacin da aka sace daliban sun tabbatar wa manema labarai aukuwar lamarin.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 731

Kazalika wani ganau ya ce an tabbatar da sace mata fiye da 300 ne sakamakon kirga dukkan ‘yan makarantar da suka rage bayan barayin sun sace daliban.

Har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar da ma gwamnatin Zamfara ba su ce komai a kan batun ba.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: