Gaskiyar Dalilin Cire Safarau Daga Kwana Casa’in


0 1,197

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

MENENE dalilin cire jarumar da ake kira Safara’u daga shirin ‘Kwana Casa’in’ na gidan talbujin na Arewa24? Majiya mai tushe ta yi wa mujallar Fim bayani.
Maye gurbin jarumar, wadda sunan ta na ainihi Safiya Yusuf, ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin masu bibiyar wannan diramar mai dogon zango da kuma ‘yan taratsi a soshiyal midiya.

 

Masu kallo sun ɗau tsawon watanni su na jiran fitowar shahararren fim ɗin mai farin jini, wanda sai a ranar Lahadi da ta gabata tashar ta dawo daga hutun wata huɗu na haska shi.
Sai dai farin cikin da jama’a su ka yi na ci gaba da haska shirin ya zo tare da kukan cewa an ga wasu sauye-sauye a shirin, musamman cire wasu jaruman da ke taka rawa a cikin sa.
Sauyin da ya fi ɗaukar hankalin su shi ne bayyanar wata sabuwar fuska wadda ta maye gurbin ɗaya daga cikin taurarin da aka fi so a kalla, wato Safara’u.
Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 321

-Advertisement-

Wasu masu kallo sun faɗa wa mujallar Fim cewa ba su ji daɗin haka ba, kasancewar jarumar ta kan yi iya bakin ƙoƙarin ta a shirin.
Rashin bayani daga tashar Arewa24 ya haifar da surutai kala-kala, wanda hakan ya sa wakilin mu ya tuntuɓi ƙwaƙƙwarar majiya mai alaƙa da shirya shirin don jin dalilin cire jarumar.
Majiyar, wadda ta buƙaci a sakaya sunan ta, ta yi bayanin cewa: “Shi tsarin fim mai dogon zango, wanda akafi sani da ‘series’, a duk duniya – ko a Bollywood ko Hollywood – ana iya cire jarumi, kazalika a mayar da wani gurbin sa ko da kuwa shi ne wanda labarin ya ginu a kan sa.

“Misali, idan mu ka yi duba a ɗaya daga cikin irin waɗannan finafinan da wannan tasha ta fara haskawa na farko, mai suna ‘Daɗin Kowa’, in za a iya tunawa zuwa yanzu an canza jarumai sama da guda biyar, kamar su Malam Musa wanda ba da shi aka fara wannan shirin ba; Furera matar Sallau; Kubura yayar Nazeer ita ma ɗora ta aka yi ta ci gaba, sannan ga matar Malam Habu; har ma da Alawiyya wadda ita ma ɗora ta aka yi ta ci gaba wanda asali ba ita ba ce ta farko.
“Haka da man tsarin fim mai dogon zango ya gada.”
A game da yadda mutane su ke kallon wannan tsari, majiyar, mai bakin da ba ya ƙarya, ta ce, “A iya cewa jama’a ba su saba ganin wannan tsarin ba kamar yadda waɗannan finafinai su ka zamto na farko-farko a wannan ƙasar, dole kuwa mutane su ga bambaraƙwai. Amma a tsarin shi wannan fim ɗin, haka ya ke a duk duniya.”
Ɗaya daga cikin surutan da mutane ke yi game da cire jarumar har da batun bayyanar wani guntun bidiyon tsiraici da ake zargin cewa ita ce a ciki, wai shi ya sa aka cire ta.
Amma majiyar ta mujallar Fim ta tabbatar da cewa  ba wannan ba ne dalilin.
Ta ce: “Yanayi ne ya sa aka canza wannan jarumar inda kamar yadda aka sani irin waɗannan tashoshi su kan ɗauki mutum ya musu aiki a kan wata yarjejeniya, kamar yadda ita ma dai a iya cewa yarjejeniyar tata ce ta ƙare, shi ya sa aka canza ta da wata. Amma ba batun da mutane su ke tunani ba ne.”
Mujallar Fim ta yi ƙoƙarin jin ta bakin jaruma mai farin jini Safiya Yusuf a kan wannan al’amari amma abin ya faskara saboda mun kasa samun ta a waya.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.