Daga Jaafar Jaafar
Wallahi an rainawa matasanmu ajawali. Shekara da shekaru ba ku ba su takardar sama musu aikin yi ba sai takardar “nomination” na kwamitin kamfe. Shi kuma shawarakin sai ya dora a fesbuk yana wage baki yana so ka ce masa “Congratulations”.
- Advertisement -
Ya kamata mu yi karatun-ta-nutsu. Idan takardar aikin CBN ne ko FIRS ko NNPC ko NLNG ko TETfund wallahi ko kyallinta ba ma gani domin ‘ya ‘yansu suke rabawa.
Kaico!