[GASA]Rarara Zai Bada Kyautar Motoci, NAPEP, Babura Da Kudi Ga Mawaka 50

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Rarara Zai Bada Kyautar Motoci, NAPEP, Babura Da Kudi Ga Mawaka 50 Da Za Su Yi Gasar Yi Wa Sabon Sarkin Kano Waƙa

Daga Aliyu El-idrith Shu’aibu.
(Dan Autan Media)

Shauƙin cire Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da maye gurbin sa da Aminu Ado Bayero ya sanya fitaccen mawaƙin nan, Dauda Kahutu (Rarara) ya saka gasa inda zai raba kujerun Makka da Umara da motoci, da kuɗaɗe kyauta ga waɗanda su ka yi nasara.

Rarara ya bayyana haka ne a wani saƙon bidiyo da ya fitar a shafin sa na YouTube.

Ya ce ya saka gasar ne don nuna farin ciki game da naɗa Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano da gwamnatin jihar ta yi.

Rarara mawaƙin siyasa ne wanda ke bin gwamnatin da ke kan mulki.

Ya ce a ƙa’idojin shiga gasar ana so duk wani mawaƙin Hausa da ya ke Nijeriya ko wajen ta da ya yi sabuwar waƙa ga sababbin sarakunan Kano guda biyar, wato na Kano da na Bichi da na Ƙaraye da na Sarkin Gaya da na Rano.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 337

A ƙa’idojin, ana so kada waƙar ta wuce minti biyar, sannan ya kasance a cikin minti biyar ɗin nan mawaƙi zai yi wa kowane sarki waƙar sa, cikin salo da zai burge kowace fada, da kuma su kan su sarakunan.

Tilas ne duk mawaƙin da zai shiga gasar ya kasance ya na da rajista da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Bugu da ƙari, mutum 50 kacal za a zaɓa a matsayin zakarun gasar.

A cewar sa, a ranar da za a fidda zakarun kowane mawaƙi zai zo da waƙar sa a rubuce kuma ya rera ta a gaban manyan baƙin da za su halarci taron, cikin su har da Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR Khadimul Islam.

Rarara ya bayyana cewa ya tanadi farfesoshin nazarin harshen Hausa da za su zama alƙalan gasar.

Ga jerin sunayen kyaututtukan da zai ba waɗanda su ka yi nasara:

Na 1: Mota
Na 2: Mota
Na 3: Kujerar Makka
Na 4: Kujerar Makka
Na 5: Kujerar Umara
Na 6: Kujerar Umara
Na 7: Keke Napep
Na 8: Keke Napep
Na 9: Babur
Na 10: Babur.

A karshe muna addu’ar Allah Ya baiwa mai rabo sa’a.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: