Gareth Bale na dab da barin Real Madrid zuwa China

1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Gareth Bale na dab da shirin barin Real Madrid zuwa kulub din China Jiangsu Suning kan yarjejeniyar shekara uku.

Wasu majiyoyi kusa da dan wasan na Wales sun tabbatar da rahotanni daga Spain da ke cewa an kusan cimma yarjejeniya, duk da cewa ba a tabbatar ba.

Tuni kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce Bale mai shekara 30 yana da dab da barin Real Madrid bayan an ajiye shi a wasan sada zumunci da Bayern Munich ta doke Madrid 3-1.

Rahotanni sun bayyana cewa Bale zai karbi kimanin fam miliyan daya duk mako a China.

Wasan da Real Madrid ta yi canjaras 2-2 da Arsenal a wasan share fagen kaka, zai kasance wasan karshe da Bale ya bugawa Madrid.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 54

A 2013 Real Madrid ta karbo Gareth Bale kan fam miliyan £85m daga Tottenham, dan wasa mafi tsada a lokacin.

Shekaru uku suka rage kwangilarsa ta kawo karshe a Bernabeu inda ya lashe kofin zakarun Turai guda hudu da Real Madrid ta lashe a 2014, 2016, 2017 da 2018.

Sannan ya lashe kofin La liga daya da Copa del Rey, da kofin Super na Uefa da kuma kofi uku gasar zakarun kungiyoyin duniya.

Gareth Bale

Idan har ta tabbata, Bale yanzu zai hadu da tsoffin ‘yan wasan gasar Premier ta Ingila da suka koma China irinsu Marko Arnautovic da Marouane Fellaini da Mousa Dembele da kuma Oscar.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: