Labarai

GANI YA KORI JI: Hakikanin Halin Da Wanda Ya Yi Batanci Ga Annabi S.A.W Yake Ciki

Daga Jamilu Sani Rarah
Wannan shine bayanin da na yi wa wasu ‘yan uwa da suka tare ni suka bukaci jin wani abu daga bakina, ganin cewa, mune farkon wayñdanda suka fara neman wannan Yaron kuma mune muka yi nasarar cafke shi.

Farko duk zafin kan da ‘yan uwa suke ji da kishin da suke ji hakika mu ma wallahi muna Jjn sa domin hatta a lokacin da muke kan nemansa Wallahi tallahi na yi kuka saboda kona ni da abin yake yi a zuciya.

Sun ce, bai kamata a tsaya bincike ba, na ce wannan kuma kuskure ne babba domin ni da su duka muna yin Facebook kuma dukan mu babu mai tabbacin cewa, gobe ko jibi ba za a iya yin hacking din account dinsa ba, yana can yana bacci a yi masa irin wannan aika aikar ba. Don haka a addinance bincike ne mataki kafin hukunci.

Mun je Nneman Yaron gidansu da kyar muka samu gane gidan, bayan mun gano sai ‘yan uwan Yaron suka ce mana wallahi ba shi da hankali tare da nuna mana cewa, ai ya saba yin irin wannan mummunan rubutun a jikin ginin gidan nasu suna gogewa (hakan ya sa suka ja ni suka nuna min na gani da idona).

Kai tsaye sai muka bukaci su ba mu Yaron sai suka ce, ai tunda baida hankali sun tura shi Asibitin Kware a nan mukayi waya da Comrd Husaini Muhammad, Comrd ya bada gudumuwa sosai wajen tabbatar da baya Asibitin kware Ashe wasu daga cikin ‘yan Uwan Yaron ne suka tura shi wani gari ba Asibitin Kware ba.

Anan Comrd Husaini ya bincika mana Kware sai ya tabbatar mana da ashe ba ya Kware sun tura shi wani wuri ne, anan muka tsoratar da su akan aikata haka da suka yi tare da nuna musu ai su kawo shi shine mafita gare su ko dukansu su samu matsala. Nan ne suka fahimce mu tare da kawo wannan Zindikin Yaron.

Daga kawo sa Wallahi na fahimci lalle ba shi da lafiya, domin yawan sumar da ke kansa da dattin da ke cikin kumbar sa kawai sun isa ka tabbatar da mahaukaci ne a gabanka.

Nan muka dauke shi muka kai shi state CID tare da Hannunta shi gare su.

Akwai abinda bai kamata In fada a Facebook ba, amma kuma ya zama dole na fada domin al’umma su san cewa, ‘yan sanda ma Masoya ne na Annabi (SAW).

Tawagar da muka je neman sa da su na ‘yan sanda ne da duk fadin jihar Sokoto ana tsoron su.

Wallahi abinda muka shirya da mun ga yana da hankali da yanzu wani labarin ake yi ba wannan ba.

Kuma na tuntubi wani daga cikin manyan malaman mu na gaya masa halin da muka ga wannan zindiki ( eh zindiki tunda ko jnjiri ya zagi Annabi wallahi ba zan tausaya masa ba balle har in kira shi da wani suna daban).

Wannan Malamin ya bada shawara mai kyau game da shi kuma In shaa Allahu idan aka bi ta duka za mu fahimci tabbas an kare martabar Annabin mu Abin Alfaharinmu.

Hakika matasanmu sun nuna kishin su sosai ga abin Alfaharinmu tare da burge ni matuka, tabbas Sokoto tana nan da sunanta Birnin Shehu.

Jinjina ga su, Farfesa Mansur Sokoto, Malam Bello Hasaan Almustapha, Sirajo Abdullahi, Dan Almajiri, Zubairu Abdullahi, Engr Bello Rabah, Comrd Husaini, Shattiman Goronyo, Zannan Goronyo, Zannan Rabah, Abbas Kwarare, Malam Imran da sauran su hakika ‘yan uwa kun nuna kokari kwarai da gaske.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: